Baza mu iya kokari ba da wannan nauyin bashin – Buhari

21

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace kasashe masu tasowa ba za su iya saka hannun jari a rayuwar bil’adama har sai sun dakile matsalolin da nauyin basussuka ke jawowa.

Shugaban kasar yace babu yadda za a yi a inganta ayyukan da ke taimakawa rayuwar al’umma gaba daya muddin kasashen suna cigaba da ware wasu kudade domin biyan basussuka.

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi ne yau a wajen taron zuba jari karo na 5 da aka gudanar a birnin Riyad na kasar Saudiyya.

A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhamadu Buhari ya ce abubuwa daban-daban ne suka haifar da kalubalen tsaro a kasarnan.

Ya yi wannan jawabi ne a jiya a yayin wani takaitaccen biki a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda jakadun tarayyar Turai da na kasashen Japan, Burundi, Denmark, Finland, Ireland, Cape Verde, Faransa, Qatar, Saliyo da Ghana suka karbi wasikun amincewa da fara aiki.

Ya ce ana bukatar karin hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen rashin tsaro a kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × four =