Ana gudanar da zaben farko a Iraqi gabannin zaben ‘yan majalisu

64

An fara kada kuri’a da wuri a zaben ‘yan majalisar dokokin Iraki, inda jami’an tsaro, fursunoni da’ yan gudun hijira suka jefa kuri’unsu kwanaki biyu gabanin babban zaben ranar Lahadi.

‘Yan Iraqi za su zabi sabuwar majalisar dokoki a karo na biyar tun bayan mamayar da kasar Amurka ta jagoranta a shekarar 2003 wanda ya hambarar da shugaban kasa Saddam Hussein.

Kimanin kujeru 329 ne za a fafata a zaben, wanda aka matso dashi daga shekarar 2022 a matsayin rangwame ga zanga-zangar neman demokaradiyya karkashin jagorancin matasa da ta barke a karshen shekarar 2019.

Amma ana sa ran masu jefa ƙuri’a da yawa za su nesanta kansu daga zaben sanadiyyar cin hanci da rashawa da shugabanci mara inganci wanda ya kasa cika burin mutane miliyan 40 na Iraki, kashi 60 daga cikinsu basu wuce shekaru 25 ba.

Akwai fargabar yawan masu kada kuri’a na iya raguwa a kasa da kashi 44.5 bisa 100 da aka yi wa rajista a shekarar 2018.

Sama da ‘yan takara dubu 3 da 240 ne ke fafatawa a zaben, ciki har da mata 950.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen − eleven =