An daure masu hawa babura 16 saboda take doka a Jigawa

38

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun cafke masu babura 16 saboda taka dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kakaba.

Kakakin ‘yan sanda na jihar, ASP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen ga manema labarai a Dutse.

Ya ce an kama masu baburan ne a Dutse saboda laifin rashin biyayya ga umarnin da gwamnatin jihar ta bayar.

Ya ce an gurfanar da masu laifin a gaban kotu sannan aka yanke musu hukuncin daurin watanni uku tare da zabin biyan tara.

SkyDaily ta bayar da labarin cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayar da umarnin takaita zirga-zirgar babura daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe a fadin jihar.

Manufar dokar ta takaita zirga-zirga ita ce magance ayyukan masu laifi a jihar.

Rundunar yansandan ta yi nuni da cewa dokar har yanzu tana nan tana aiki, inda ta shawarci sauran jama’a da su kiyaye ta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 10 =