An dakatar da jigilar jiragen kasan Kaduna-Abuja bayan harin ‘yan bindiga

15

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kan jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, lamarin da ya tilasta wa jirgin ya tsaya a tsakiyar hanya.

An raiwaito cewa yan bindigan sun fara kai farmaki kan jirgin a jiya da daddare kuma sun samu nasarar tsayar da shi.

‘Yan bindigar, a cewar majiya, sun sake dawowa da safiyar yau, inda suka dasa nakiyoyi akan hanyar jirgin kasa.

Wani ma’aikacin Hukumar Jiragen Kasa da ya nemi a sakaye sunansa, ya sanar da cewa sun fuskanci harbe-harbe, kuma jirgin ya tsaya yayin da harbe-harben suka lalata tankin mai.

Hukumar Jiragen Kasa kazalika ta tabbatar da cewa nakiyoyin da aka dasa sun tashi akan hanyar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, amma ba a san wadanda suka dasa ba.

Manajan daraktan hukumar, Fidet Okhiria, wanda ya zanta da manema labarai ya bayyana cewa abubuwan fashewar sun lalata digar jirgin.

A wani labarin mai alaka da wannan, Hukumar Jiragen Kasa ta dakatar da ayyukan jirgin kasa a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumar ta dauki wannan matakin ne bayan lalata hanyar jirgin kasan.

A cikin wata sanarwa a yau a shafinta na internet, hukumar tace an dakatar da jigila a hanyar jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, don kare lafiyar fasinjoji da ma’aikatan jirgin.

A cewar hukumar, ana kokarin tabbatar da cikakken tsaro a kan hanyar.

Hukumar ta kara da cewa za a sanar da karin haske game da dakatarwar zuwa ga jama’a, nan ba da jimawa ba.

A wani labarin kuma, daruruwan fasinjojin sun makale a tashar jirgin kasa ta Rigasa da ke Kaduna a safiyar yau.

Fasinjojin sun rasa jirgin kasan da zasu hau zuwa Abuja sanadiyyar harin da ya auku.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four × three =