‘Yan fashin daji sun sace dalibai a Maradun ta jihar Zamfara

170

‘Yan fashin daji sun sace daliban makarantar sakandiren jeka ka dawo ta Kaya a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Har yanzu babu cikakken bayani dangane da lamarin amma ance ‘yan fashin dauke da makamai sun kutsa kai cikin makarantar a yau da safe.

Wani mazaunin garin ya gayawa manema labarai cewa ‘yan fashin dajin sun mamaye makarantar da misalin karfe 11 da rabi na safe, lokacin da daliban ke rubuta jarabawa.

Har yanzu ba a san adadin daliban da aka sace ba amma akwai yiwuwar dalibai mata da aka sace sun fi maza yawa, kasancewar makarantar ta maza da mata ce.

Lamarin yazo ne kwanaki kalilan bayan wasu dalibai da aka sace sun samu yanci.

Maradun ne garin gwamnan jihar, Bello Matawalle kuma wata majiya mai tushe daga gidan gwamnati a Gusau tace an sanar da gwamman batun sace daliban kuma yana gudanar da zaman ganawar tsaro dangane da lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five − 4 =