Tsohon dan majalisar Malawi ya harbe kansa a majalisar

41

Tsohon dan majalisar Malawi Clement Chiwaya ya kashe kansa ta hanyar Harbin bidiga, a cikin ginin majalisar kasar.

Chiwaya wanda yake amfani da keken masu matsalar kafafu, tun yana dan shekara b2 bayan kamuwa da cutar Polio, ya taba rike matsayin mataimakin kakakin majalisar.

A wani sako da ya bari kafin ya je majalisar, ya rubuta rikicin da ke tsakaninsa da majalisar kan takaddamar mallakar mota.

Bayan ya fadi zabe sai ya yi ta kokarin sayan wata mota da aka ba shi wadda ke ba shi damar tuki duk da matsalar kafafu da yake fama da ita.

Ya biya kudin motar amma ya zargi majalisar da gaza ba shi damar mallakar motar.

Cikin wata sanarwa da aka fitar bayan mutuwar tsohon dan majalisar, ofishin kakakin majalisar yace maganar tana gaban kotu.

Jaridun kasar sun ruwaito cewa ya shiga ofishin magatakardar majalisar a yau sannan ya harbe kansa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen + fourteen =