Shugaban Kasar Tunisia Kais Saied ya nada Najla Bouden Romdhane, wata injiniyar jami’a wacce ya yi aiki tare da Bankin Duniya, a matsayin Firai Ministar mace ta farko, kusan watanni biyu bayan ya kwace mafi yawan madafun iko a wani mataki da makiyansa ke kira juyin mulki.
Romdhane za ta hau kujerar mulki a lokacin da kasar ke fama da rikici, tare da nasarorin dimokradiyya da aka samu a juyin juya halin shekarar 2011 ke cikin shakku da kuma babbar barazanar dake tunkarar arzikin kasa.
Kais Saied ya kori Firayim Minista na baya, ya dakatar da Majalisar kuma ya kwace madafun iko a watan Yuli, kuma yana fuskantar matsin lamba na cikin gida da na kasashen waje don kafa sabuwar gwamnati.
A makon da ya gabata ya yi watsi da yawancin kundin tsarin mulkin kasar inda ya ce zai iya yin mulki ta hanyar dokar soja.
Ya nada Romdhane a karkashin tanade-tanaden da ya sanar a makon da ya gabata kuma ya nemi ta gaggauta kafa sabuwar gwamnati.