Wani dan majalisar dokokin jihar ta Sokoto mai suna Saidu Ibrahim, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihoshi da su ceto mazabar Sokoto ta Gabas daga hannun ‘yan bindiga masu dauke da makamai.
Dan majalisar ya ce a shirye yake ya jagoranci sojoji zuwa maboyar ‘yan fashin dajin, a duk lokacin da suke so su je domin fuskantar su.
Sa’idu Ibrahim, wanda ke wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a majalisar dokokin, ya ce a yanzu haka ‘yan bindiga ne ke da iko da mazabarsa.
Da yake zantawa da manema labarai a hira ta wayar tarho, Saidu Ibrahim ya ce ba zai iya komawa mazabarsa ba saboda ‘yan fashin dajin sun mamaye ta.
Dan majalisar ya ce ya ga daruruwan sojoji a cikin motoci amma ba sa gudanar da sintiri a yankunan da ‘yan bindigar suke.
Sa’idu Ibrahim ya ce shi da dan majalisa mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Boza; da tsohon shugaban karamar hukumar, Idris Danchadi, zasu jagoranci sojojin zuwa inda ‘yan fashin suke.