Majalisar wakilai za ta binciki hauhawar farashin abinci

80

majalisar wakilai ta kafa wani kwamiti na musamman da zai binciki tsadar kayayyakin abinci da kayayyakin masarufi a fadin kasarnan.

Kwamitin wanda aka kafa a jiya zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar, Peter Akpatason daga jihar Edo.

Kafa kwamitin ya biyo bayan amincewa da bukatar hakan da dan majalisa Ibrahim Isiaka daga jihar Ogun, ya gabatar.

Babban aikin kwamitin shi ne kaddamar da sauraron jin ra’ayin jama’a tare da dukkan masu ruwa da tsaki a kasar nan da kuma gudanar da bincike kan musabbabin hauhawar tsadar rayuwa.

Da yake gabatar da kudirin, Ibrahim Isiaka ya ce farashin kayayyakin abinci sun yi tashin gwauron zabi da kashi 100 a sassa da dama na kasarnan, cikin shekara guda da ta gabata.

Ya dora alhakin tsadar kan manufofin kudi da sauran manufofin kasafin kudi na gwamnati, gami da rufe iyakokin kasarnan hade da matakan dakile cutar corona da kuma rashin tsaro.

A wani labarin kuma, yan majalisar wakilai a yau sun nemi gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Babajimi Benson ne ya gabatar da kudiri a zauren majalisar inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan fashin daji a matsayin ‘yan ta’adda.

A kudirin nasa, Babajimi Benson ya ce matakin zai nuna jajircewar gwamnatin tarayya wajen yakar manyan laifuka da kashe-kashen da ‘yan bindiga ke yi a fadin kasarnan.

Ya lura cewa hakan zai zama abin karfafa gwiwa ga sojoji a yakin da su ke yi da batagari a yankin.

Ya sanar da cewa a ayyana neman dukkan sanannun ‘yan bindiga ruwa a jallo, kuma a kama su a duk inda aka same su don hanzarta yanke musu hukunci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 4 =