Babbar kotun shari’ar musulunci ta Jihar Kano ta ki amincewa da bayar da belin Sheik Abduljababr Nasir Kabara.
A zaman na yau, sabbin lauyoyin da ke kare Abduljabbar Kabara, karkashin jagorancin Barista Muhammad Umar, sun nemi a bayar da belin nasa bisa dalilin cewa iyalansa na fuskantar matsaloli sakamakon daure shi.
Barista Muhammad Umar ya kara da cewa idan aka bayar da belin wanda ake tuhuma, yana iya samun lokacin kare kansa kamar yadda ya kamata.
Lauyoyin masu gabatar da kara, wanda Suraj Saida ke jagoranta, sun nuna adawa da rokon belin lauyan Abduljabbar, inda suka yi nuni da cewa laifin babban laifi ne wanda ba a bayar da belinsa.
Alkalin kotun Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, ya ki amincewa da bukatar bayar da belin nasa, inda ya dage saurar karar zuwa ranar 14 ga watan Oktoban gobe.