Gwamnati ta amincewa ma’aikata maza suke tafiya hutun haihuwa

68

Taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a yau ya amince da hutun haihuwa ga ma’aikatan gwamnatin tarayya a kasarnan.

Da yake yi wa manema labarai karin haske bayan taron Majalisar da aka gudanar a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta yi bayanin cewa daga yanzu, ma’aikatan gwamnatin tarayya maza za su cancanci hutun haihuwa na kwanaki 14 kamar takwarorinsu mata.

Ta ce, an yi hakane don bayar da damar inganta alaka tsakanin uba da jariri musamman a farkon matakin rayuwar jaririn, wanda har zuwa yanzu ma’aikatan gwamnati mata ne kawai ke cin moriyar hakan.

Yemi-Esan ta cigaba da bayanin cewa iyaye maza da suka dauki nauyin rikon jariri dan kasa da wata hudu suma za su ci gajiyar wannan karimcin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three − one =