Buhari ya kori ministoci biyu daga gwamnatinsa

52

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tsige ministan aikin gona, Muhammad Sabo Nanono, da takwaransa na wutar lantarki, Saleh Mamman.

Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya sanar da haka a yau a wajen taron manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Yace ministan muhalli, Mohammed Mahmud Abubakar, ya maye gurbin Sabo Nanona, yayin da karamin ministan ayyuka da gidaje, Abubakar Aliyu, ya maye gurbin Saleh Mamman.

Shugaban kasar yace canje-canjen ya biyo bayan al’adar gwamnatinsa ta bibiyar shirye-shirye da aiwatar da tsare-tsare, ta hanyar amfani da rahotanni a wajen zaman majalisar zartarwa da kuma guraren taruka.

Saleh Mamman dan jihar Taraba ne, yayin da Sabo Nanona ya fito daga jihar Kano.

Ba a san Buhari da sauke ministoci ba. A lokacin wa’adin mulkinsa na farko daga shekarar 2015 zuwa 2019, ministocin da suka bar gwamnatinsa, sun sauka ne bisa radin kashin kansu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 3 =