‘Yan Bindiga sun kashe mutane 47 a Burkina Faso

52

A kalla mutane 47 ne suka mutu cikin har da fararen hula a arewacin kasar Burkina Faso, a wani taho mu gana da aka yi tsakanin masu ikirarin jihadi da dakarun gwamnati.

Wasu mutum 19 na daban kuma sun jikkata bayan wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne suka farwa tawagar wasu fararen hula da sojoji ke yi wa rakiya a jiya.

Ma’aikatar yada labarai ta kasar ta bayyana cewa sojoji 14 da wasu masu aikin sakai sun mutu.

Sojojin gwamnati sun ce sun kashe mutane 58 a wani mataki na daukar fansa, sun kuma jikkata wasu da yawa da ba a san adadinsu ba.

Tun a shekarar 2015, Burkina Faso ke fuskantar hare-haren masu ikirarin jihadi abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, dubbai kuma suka gudu suka bar muhallansu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya tilasta wa sama da mutumane dubu 17 barin kasar tun daga farkon wannan shekarar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

seven − two =