Tsohon shugaban Chadi Hissene Habre ya rasu

35

Tsohon Shugaban Kasar Chadi Hissene Habre ya rasu a yau yana da shekara 79 a duniya.

Hissene Habre ya rasu ne a asibiti yayin da yake zaman gidan yari a Senegal bisa aikata laifukan yaki da kuma lalata rayuwar ‘yan Adam.

Wata kafar yada labarai ta Senegal ta ce ya rasu ne sakamakon cutar korona.

A cewar masu bincike, a lokacin da ya mulki Chadi tsawon shekara takwas, shugaban ya dinga murkushe ‘yan adawa, abin da ya jawo mutuwar mutane fiye da dubu 40.

An kuma zarge shi da fyade, da cin zarafin mata da bayar da umarnin kisan kai a lokacin da yake mulki. Sai dai, ya musanta hakan.

A shekarar 2016 ne wata kotu ta musamman, wacce kungiyar hadin kan Afirka (AU) da Senegal suka kafa, ta yanke masa hukuncin daurin rai-da-rai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 13 =