Najeriya baza ta zama kamar Afghanistan ba – Lai Mohammed

43

Ministan Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce Najeriya ba kasa ce da ta gaza ba kuma ba za ta iya bin tafarkin Afghanistan ba inda ‘yan Taliban suka karbe iko.

Ministan ya bayyana hakan ne a birnin Washington DC na Amurka, yayin ganawarsa da hukumomin kafafen yada labarai na duniya da suka hada da Gidan Rediyo da Talabijin na BBC da Bloomberg da Politico.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya bayar da rahoton cewa ministan yana kasar Amurka don ganawa da kungiyoyin kafafen yada labarai na kasa da kasa akan nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kokarin da take yi zuwa yanzu na magance tashin hankali, fashi da makami da kowane irin laifi.

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawar da ya yi da hukumomin kafafen yada labaran uku, Lai Mohammed ya ce rade-radin cewa yanayin tsaro a Najeriya na iya tabarbarewa zuwa na Afghanistan ba daidai ba ne.

Ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya tana samun nasara a yakin da ake yi da ta’addanci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine − nine =