Mutane 85 sun mutu a harin filin jiragen sama a Afghanistan

99

Akalla fararen hula 72 ne suka mutu sakamakon fashewar bama -bamai guda biyu a wajen filin jirgin saman Kabul dake Afghanistan.

Akalla sojojin Amurka 13 ne suka rasa rayukansu a fashe-fashen na jiya, mafi munin asarar rayuka cikin kwana guda ga sojojin Amurka a Afganistan tun bayan harin da aka kai kan jirgin sama mai saukar ungulu na Chinook a watan Agustan 2011 wanda ya kashe sojoji 30.

Sojojin Amurka da ke taimakawa kwashe ‘yan Afghanistan da ke son guduwa daga mulkin Taliban, suna taka-tsantsan saboda yiwuwar samun karin hare-hare.

Kungiyar IS mai da’awar kafa daular Islama a lardin Khorasan ta ce ita ce ta kai harin na jiya, inda ta ce ‘yan kunar bakin waken sun nufi masu fassara da masu hadin gwiwa da sojojin Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi alkawarin mayar da martani kan harin da aka kai a Kabul, inda ya tabbatar da cewa kungiyar ISIS ce ta kai harin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − four =