Hukumar kula da yanayi ta kasa (NiMet) tace cikin kwanaki uku masu zuwa, akwai yiwuwar za a samu ruwan sama mai karfin gaske a jihohin Katsina da Jigawa da Neja da Kogi da Nasarawa da Benue da Cross River.
Hukumar ta bayyana cewa akwai yiwuwar a fuskanci matsakaicin ruwan sama ko mai yawa a wasu yankunan Jihohin Sokoto da Kano da Zamfara da Bauchi da Ebonyi da Enugu da Abia da Akwa Ibom daga yau zuwa Juma’a.
A gefe guda kuma, za a iya fuskantar matsakaicin ruwan sama a yankunan jihohin Rivers da Kwara da Delta da birnin Abuja da arewacin Kaduna.
Hukumar ta yi gargadin cewa sakamakon hasashen ruwan sama kamar da bakin kwarya da za a samu cikin kwana uku masu zuwa, akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a kan tituna da gidajen da ke cikin kwari da koramu da kuma koguna.