Kungiyar masu adawa da Taliban sun shirya fada

27

Wata kungiyar adawa ta ce tana da dubban mayaka da ke shirye don fafata yaki da Taliban wadda ke iko da mafi yawan Afghanistan.

Ba a tabbatar da ingancin wannan ikirari ba, wanda kakakin kungiyar ta NRF mai suna Ali Nazary ya yi.

Nazary ya fadawa manema labarai cewa NRF na da dubban mayaka da ke cikin shirin yaki amma za su nemi tattaunawar sulhu tukunna.

A cewarsa idan sulhun ya Gagara, kungiyar baza ta yarda da kowace irin tsokana ba,

Kalaman nasa na zuwa ne bayan Taliban ta ce ta kewaye yankin Panjshir, inda nan ce maboyar mayakan.

Shugabannin kungiyar sun ce Taliban na cigaba da tunkarar yankin wanda ke arewa maso yammacin birnin Kabul.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =