Jami’ar Sule Lamido Kafin Hausa ta dauki sabbin dalibai 1,086

294

Jami’ar Sule Lamido ta Kafin Hausa, ta rantsar da sabbin dalibai dubu 1 da 86.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Lawan Sani Taura ne ya bayyana hakan a jiya yayin bikin rantsar da sabbin daliban da za suyi karatun digiri na farko na jami’ar na shekarar karatu ta 2020/2021.

A cewar Mataimakin Shugaban Jami’ar, jimillar dalibai dubu 1 da 86 aka dauka domin karatu a kwalejojin jami’ar guda uku, ta hanyar jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta JAMB.

Farfesa Lawan Taura ya umarci sabbin dalibai da suyi amfani da fa’idar shigarsu Jami’ar don bunkasa kawunansu ta fuskar dabi’u masu kyau da ilimi, don zama mutane nagari a cikin al’umma.

Magatakardar Jami’ar ne ya jagoranci rantsar da sabbin daliban.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

2 × 3 =