Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da kwamitin cikar Najeriya shekaru 61

24

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai 12 na ministoci, don tsara bikin cikar Najeriya shekaru 61 da samun ‘yancin kai.

Da yake kaddamar da kwamitin jiya a Abuja Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce manufar fara shirye-shiryen da wuri shine domin a cimma burin da aka sanya a gaba.

Kwamitin karkashin jagorancin Boss Mustapha, yana da Ministocin Watsa Labarai, da na harkokin cikin gida, da na Babban Birnin Tarayya, da na Zuba Jari, Kasuwanci da Masana’antu, da Ministan Lafiya, da Babban Sufeto Janar na ‘Yan sanda, da Darakta Janar na DSS, a matsayin membobi.

A cewar Boss Mustapha, ayyukan da aka gabatar don bikin cika shekaru 61 sun hada da kammala ayyukan bikin cikar Najeriya shekaru 60, wanda suka hada da ibadar coci a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba da Sallar Juma’a a ranar Juma’a, 1 ga watan Oktoba da kuma bikin bayar da kyaututtuka da za ayi a ranar Lahadi, 3 ga watan Oktoba.

Hakanan, Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, Niyi Adebayo, wanda shine shugaban karamin kwamitin, yayi karin haske cewa tuni kwamitin ya kafa wakilansa don gudanar da gagarumin biki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 − 6 =