Gwamnatin Tarayya ta fara shirin zaben sabon CG na Immigration

56

Gwamnatin tarayya ta fara shirin zaben sabon shugaban hukumar shige da fice ta kasa, immigration.

Shugaban hukumar mai ci, Muhammad Babandede, zai bar aiki nan bada dadewa ba, kasancewar wa’adin da aka kara masa a bara, yazo karshe.

Babandede, wanda ya fito daga Jihawa Jigawa, shine ma’aikacin da yafi kowa dadewa a hukumar, kasancewar ya fara aiki da hukumar a watan Yunin 1985.

Shugaban mai barin gado, ya aika da sunayen mataimakansa su 10 ga hukumar kula da civil defense, gidajen gyaran da’a, shige da fice da ta kashe gobara, domin zaben shugaban hukumar na gaba.

Hakan na kunshe cikin wata wasika da Babandede ya aikawa kwamitin zaben sabon shugaban hukumar, mai dauke da kwanan watan 9 ga watan da muke ciki, wacce manema labarai suka samu a jiya.

Ana sa ran kwamitin zaben zai zakulo manya daga cikin mataimaka 10 ya aikawa hukumar domin zaben sabon shugaba, kafin amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

nine + fifteen =