Gwamnatin Tarayya ta ba wa Katsina N6.25bn domin kiwon shanu

75

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya tabbatar da cewa jihar ta karbi naira biliyan 6 da miliyan 250 daga gwamnatin tarayya domin aikin guraren kiwo.

An fito da aikin ne don magance rikicin manoma da makiyaya wanda ya rikide zuwa rikicin ‘yan fashin daji a jihohin Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya.

Gwamna Masari ya tabbatar da karbar kudaden a jiya yayin da yake gabatar da lacca kan shugabanci, tsaro da cigaba mai dorewa a Afirka, a cibiyar nazarin tsaro ta kasa dake Abuja.

Ya kara da cewa jihohi ne suka fara aikin kuma suka tuntubi gwamnatin tarayya don neman taimako.

Gwamnan ya ce aikin ya kunshi gina hanyoyin, da mahauta da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da ofisoshin ‘yan sanda a wuraren kiwon.

Aminu Masari ya ce aikin ya kuma hada da gyaran ababen more rayuwa da suka hada da madatsun ruwa da makarantu da dakunan shan magani da asibitin dabbobi, da sauransu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

19 + 8 =