Buhari ya nada Harry a matsayin shugaban hukumar kididdiga ta kasa

14

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Simon Harry a matsayin sabon shugaban hukumar kididdiga ta kasa (NBS).

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa jiya data fito daga hannun Yunusa Abdullahi, mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga Ministar Kudi, Kasafi da Tsare -Tsaren Kasa, Zainab Ahmed.

Simon Harry zai gaji shugaban hukumar Yemi Kale, wanda wa’adin mulkinsa na biyu na shekaru biyar ya kare a ranar 16 ga Augusta.

A halin yanzu, Simon Harry shine daraktan shirye-shiryen da sashen fasaha na hukumar kididdiga ta kasa, kuma ya shafe kusan shekaru talatin yana aiki da hukumar.

Ya fara aiki a hukumar kididdiga ta kasa a matsayin a shekarar 1992 kuma ya kai matsayin babban darakta a shekarar 2019.

A cikin ayyukan da yayi, ya bayar da gudummawa ga shirye- shirye da sauye-sauye da dama ciki har da gyare-gyare na ayyukan hukumar kididdiga ta kasa tare da canjin sunan hukumar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

thirteen + four =