‘Ka da ku sake ku saki sirrikan gwamnati’, Fadar shugaban kasa ta gargadi ma’aikata

37

A wani taron bada rantsuwa ga ma’aikatan fadar shugaban kasar Najeriya su 42, babban sakataren fadar shugab kasa Tijjani Umar, ya gargadi ma’aikatan akan rike sirri.

Wanda ya bada rantsuwa yayin taron, shi ne; jojin babbar kotun birnin tarayya, Mai shari’a Hamza Mu’azu. Taron ya guda ne a babban dakin taro na fadar shugaban kasa.

Da ya ke bayani akan makasudin taro, Umar ya bayyana cewa;

“Wannan shi ne mafarin duk wani aikin dai-dai a dukkan ofisoshi. Dole ne amfani da doka da ka’ida wurin aiki, wanda yi mu su karan-tsaye zai janyo hukunci. Daga yanzu dukkan ku kuna kan kulawa da sa idanun mu. Za mu hi diddigin kowa,”

Haka zalika Umar ya ja kunnen ma’aikatan, lallai gwamnati ba zata zuba ido ba ga dukkan masu sakin bayanen gwamnati na sirri. Ya ci gaba da cewa “ bayanan sirri da makamantansu dole ne ma’aikata suyi aikin da su cikin kulawa.”

Umar ya ci gaba da cewa “Kuma karya wadan nan sharadai baya cikin rukunan aiki. Don haka ne mu ka tara ku a nan mu baku rantsuwar rike sirri, mu kuma bayyana muku irin bayanan da kuke ta’ammali da su da kuma abinda zai iya biyo baya ga duk wanda ya saba shatuda da dokokin.”

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × 5 =