Hatsarin mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane 7

114

Mutane 7 sun mutu a wani hatsarin mota da ya auku a garin Tilden Fulani, dake kan babban titin Bauchi zuwa Jos a jihar Bauchi.

An rawaito cewa hadarin, wanda ya rutsa da wata koriyar mota kirar Opel, ya auku ne lokacin da sitiyari ya kwacewa direban motar kuma ta fada kogi bayan wani mamakon ruwan sama.

Wani mazaunin Tilden Fulani, Saleh Musa, ya gayawa manema labarai cewa mamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin kwarya a karshen mako ne ya haifar da lamarin.

Advertisement

Rundunar yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Kakakin rundunar, Ahmed Wakili, yace ana cigaba da bincike domin gano sauran fasinjoji 5 da suke cikin motar.

Kakakin yace an mika gawarwakin mamatan ga iyalansu domin a binne su.

Advertisement

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

18 − 18 =