Gwamnatin Tarayya ta fara ginin layin dogo daga Kaduna zuwa Kano

67

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara aikin shimfida titin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano a ranar Alhamis.

Babbar sakatariya a ma’aikatar sufuri, Magdalene Ajani, ta sanar da haka a yau cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

Sanarwar da fito ta hannun daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar ta sufuri, Eric Orjiekwe, tace za’a gudanar da bikin kaddamarwar a Zawaciki dake yankin karamar hukumar Dawakin Kudu ta jihar Kano da misalin karfe 10 na safe.

A cewar babbar sakatariyar, aikin zai kara habaka shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na hada biranen kasarnan da hanyar jirgin kasa domin inganta cigaban tattalin arzikin kasa.

Babbar sakatariyar ta kara da cewa an gayyaci manyan masu ruwa da tsaki a bangaren sufuri domin halartar bikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + fifteen =