Hukumomi a Saudiyya sun kare matakin da suka dauka na takaita sautin amsa-kuwwa a masallatai.
Ma’aikatar Harkokin Addini ta sanar a makon jiya cewa za a rage karar dukkan amsa-kuwwar da ke masallatan kasar zuwa kashi daya cikin uku na kararsu.
Ministan Ma’aikatar Abdullatif al-Sheikh ya ce sun dauki matakan ne bayan an kai musu korafe-korafe game da yadda masallatan suke kure amsa-kuwwa, lamarin da ke damun jama’a.
Sai dai matakin ya jawo kakkausan suka a shafukan sada zumunta.
Lamarin ya sa an kirkiri maudu’in da ke kira a haramta amfani da kida da waka masu karfi a wuraren sayar da abinci da shan shayi a kasar.
Al-Sheikh ya ce mutanen da suka yi korafi sun hada da iyayen da ke cewa amsa-kuwwar suna hana ‘ya’yansu barci.