INEC ta kirkiri sabbin rumfunan zabe 56,872

22

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a yau tace ta cire rumfunan zabe daga guraren da basu dace ba, da guraren ibada a fadin kasarnan.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ya sanar da haka a wata ganawa da kwamishinonin zabe na hukumar a Abuja.

A wajen ganawar, ya kaddamar da guraren sabbin rumfunan zabe guda dubu 56 da 872 da aka kirkira, tare da sanar da wasu shirye-shiryen zabe.

Bayan kirkirar sabbin rumfunan zaben, a yanzu Najeriya na da rumfunan zabe tsayayyu guda dubu 176 da 846, kari daga wadanda ake dasu a baya guda dubu 119 da 974 a jihoshin kasarnan 36 da babban birnin tarayya, Abuja.

Ya bayyana cewa jumillar rumfunan zabe 749 aka fitar daga guraren da basu dace ba.

Shugaban hukumar yace daga yanzu an dena amfani da rumfunan zabe na wucin gadi a Najeriya.

A wani labarin kuma, hukumar ta INEC ta tsayar da ranar gudanar da zaben Gwamnan jihar Osun na shekarar 2022.

Kamar yadda yazo a sanarwar hukumar wacce ta bayar da bayanin jadawali da abubuwan da za a gudanar a zaben gwamnan jihar Osun, an tsayar da ranar 16 ga watan Yulin 2022 domin zaben.

Jadawalin, dauke da sa hannun sakatariyar hukumar ta INEC, Rose Oriaran-Anthony, tace za a fara sanarwar zabe da sauran shirye-shirye gudanar da zabe a ranar 15 ga watan Fabrairun 2022.

Tace jam’iyyun siyasa zasu fara karbar takardun cikewa daga shafin internet na INEC a ranar 16 ga watan Fabrairun 2022, inda ta kara da cewa an ware ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa 12 ga watan Maris na 2022 domin jam’iyyun siyasa su gudanar da zabukan cikin gida tare da sasanta rikice-rikice da zasu iya tasowa bayan zabukan.

Sanarwar ta kuma lissafa ranar 25 ga watan Maris na 2022 a matsayin ranar wallafa bayanan yan takara, da ranar 8 ga watan Aprilu a matsayin ranar karshe ta janyewa ko maye gurbin ‘yan takara daga jam’iyyun siyasa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 + 4 =