Gwamnatin Tarayya za ta kara ciwo basuka daga China

19

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirye-shiryenta na kara ciyo bashi daga kasar China a kokarinta na fadada hanyoyin jiragen kasa a karin jihoshin kasarnan.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya sanar da haka a yau lokacin da aka zanta da shi a gidan talabijin na Arise TV, mako guda bayan yace gwamnati zata ciyo bashi daga bankin standard ba daga kasar China ba.

Amaechi bai ambaci adadin kudaden da gwamnati zata ciyo bashi ba amma yace tuni gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa.

China tana bin Najeriya bashin dala miliyan dubu 3 da miliyan 400 ya zuwa ranar 31 ga watan Maris, kamar yadda ofishin kula da basuka na kasa ya sanar.

A makon da ya gabata, gwamnati ta sanar da aniyarta ta ciyo bashin kudade domin gina wasu muhimman hanyoyin jiragen kasa, inda tace za a ciyo bashin daga bankin standarda ba kasar China ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

four + 8 =