Gwamna Matawalle ya jajantawa iyalan marigayi Ardo, ya ba da gudummawar abinci da kudi

47

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Mohammed ya jajantawa iyalan Marigayi DSP Abdulkadir Abubakar Ardo wanda ya rasa ransa kwanannan a bakin aiki a jihar Kebbi.

Gwamnan, wanda ya tura wata tawaga mai karfin gaske karkashin jagorancin Mashawarci na Musamman kan Harkokin Tsaro, Mamman Tsafe, ta kuma hada da Mashawarci na Musamman kan wayar da kan jama’a, Kafafen Yada Labarai da Sadarwa, Zailani Bappa, da sauransu.

Mamman Tsafe ya bukaci iyalan mamacin da su yi hakurin jure rashinsa tare da tuna musu cewa dukkan mai rai, mamaci ne. Ya kuma bayyana marigayi Ardo a matsayin jarumi mai kwazo da jajircewa.

A nasa jawabin, Mai bawa Gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Zailani Bappa ya kuma bukaci iyalan mamacin da suyi hakurin jure rashinsa. Inda ya sanar da tallafin kudi naira miliyan 2 da buhunan shinkafa goma masu nauyin kilogram 50 ga iyalan mamacin.

Marigayi Ardo shi ne shugaban wata tawagar ‘yan sanda ta musamman wanda ya samu rauni sannan ya mutu sakamakon harbin bindiga yayin da ya yi arangama da wasu gungun ‘yan fashin daji a kauyen Tsamiya da ke karamar Hukumar Bagudo a Jihar Kebbi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

20 − 6 =