Gwamna Badaru ya sanya hannu akan sabon daftarin cigaban Jigawa

73

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya rattaba hannu kan sabon daftarin manufofin cigaba wanda aka amince da shi bayan tattaunawa tsakanin Gwamnatin Jihar Jigawa da jami’an ofishin cigaban kasashen waje na Birtaniya a gidan gwamnati dake Dutse.

Da yake magana kafin sanya hannu kan daftarin, Gwamnan yace jihar ta samu nasara matuka wajen cimma burin daftarin da aka yi aiki da shi a baya.

Badaru Abubakar ya bayyana cewa da wannan sabon daftarin, jihar za ta hada kai da masu hadin gwiwar cigaba domin aiwatar da shi gaba daya kuma ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai an cimma burin da aka sanya a gaba, wanda ke da nufin isar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar jihar Jigawa.

Da yake mayar da martani, Daraktan Ofishin cigaban kasashen waje na Birtaniya, Dokta Chris Pycroft, ya ce sun amince da Gwamnatin Jihar Jigawa kan tsarin aiki tare wanda zai karfafa dangantakar gwamnatocin biyu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten + thirteen =