Buhari ya nada Kingibe a matsayin jakadan tafkin Chadi

27

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babagana Kingibe, a matsayin jakadansa na musamman zuwa kasar Chadi da yankin tafkin Chadi.

Sakataren gwamnatin tarayya mai ci, Boss Mustapha, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

A cewarsa, sauran nauye-nauyen da aka dorawa Babagana Kingibe sun hada da dabbaka duk wani shirin dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar Chadi, da Arewa Maso Gabashin Najeriya da kuma yankin tafkin Chadi.

Boss Mustapha yace Shugaba Buhari, ta hanyar wannan nadin, ya nuna jajircewar Najeriya wajen jagorantar yunkurin tsaron da zai kawo daidaito da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi.

Ya kara da cewa matakin zai dawo da zaman lafiya a tafkin Chadi tare da murkushe kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabas.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

14 + five =