Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da fara aiki a hukumar kula da tsofaffin kasa. Kazalika, ya kuma amince da kafa kwamitin gudanarwa mai wakilai 12 na hukumar, ba tare da bata lokaci ba.
Hakan ya fito ne ta cikin sanarwa a jiya daga hannun babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman akan kafafen yada labarai da hulda da jama’a, Mallam Garba Shehu.
Sanarwar ta yi bayanin cewa hukumar kula da dattawan za take kula da bukatun wadanda suka manyanta, masu shekaru 70 zuwa sama, ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa da inganta rayuwarsu.
Shugaba Buhari ya kuma nada Muhammad Muhammad a matsayin shugaban hukumar.
Shugaban kasar ya kuma amince da nadin Ahmed Habib, a matsayin sabon darakta janar na hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) wanda zai maye gurbin Muhammad, wanda a yanzu shine shugaban hukumar kula da dattawa.
Dukkan nade-naden na da wa’adin shekaru 4 na farko.