Buhari ya bukaci majalisa ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudi

23

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar kasa ta amince da kwarya-kwaryar kasafin na naira biliyan 895.

Bukatar shugaban kasa na kunshe cikin wata wasika da aka aikawa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, wanda ya karanta ta a farkon zaman majalisar na yau.

Bukatar ta shugaba Buhari ta zo ne kimanin makonni biyu bayan majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kudin.

Kwarya-kwaryar kasafin kudin, a cewar gwamnatin tarayya, an shirya shi musamman saboda habaka kokarin sosoji da hukumomin tsaro wajen dakile rashin tsaro daban-daban a kasarnan.

A wani bangare na samar da kudaden kasafin kudin, majalisar zartarwa ta tarayya ta kuma amince ciro kudade daga basukan bankin duniya wanda ya kai kimanin naira biliyan 39 da miliyan 580.

Majalisar dattawar za ta amince da kasafin kudin a wani zaman, bayan kwamitin da abin ya shafa ya amince da bukatar shugaban kasar.

A wani lamarin mai alaka da wannan, Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya kokari sosai ba a zangon mulkinsa na farko saboda rashin jituwar da ke tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa.

Duk da kasancewar jam’iyyar APC ce ke da iko da majalisun kasa tsakanin 2015 zuwa 2019, gwamnatin Buhari bata samu abinda take so daga majalisun ba.

Dukkan majalisun biyu karkashin jagorancin Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Kakakin Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara, suna ta takun saka da fadar shugaban kasa.

Bukola Saraki da Yakubu Dogara sun yi kaura zuwa jam’iyyar PDP mai adawa, kafin karshen wa’adin mulkin Buhari na farko.

Da yake jawabi a jiya a wajen taron matasan jam’iyyar APC, Ahmed Lawan yace jam’iyyar APC ta yi asarar shekaru 4 wadanda ya kamata ace anyi amfani da su wajen tabbatarwa da ‘yan Najeriya sun yi daidai da suka kawar da jam’iyyar PDP.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten + three =