‘Yan bindiga sun kone wasni ofishin ‘yansanda a Abia

23

Wasu batagari sun kone wani ofishin yansanda a yankin karamar hukumar Bende ta jihar Abia.

An gano cewa wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun tunkari ofishin yansandan da sanyin safiyar yau Alhamis.

Ance maharan sun kone dukkan motocin da aka ajiye a ofishin kafin su cinnawa ginin wuta.

Ofishin yansandan na zaune ne a kofar fita daga helkwatar karamar hukumar.

Lamarin ya auku kasa da awanni 6 bayan Gwamnan Jihar ta Abia, Okezie Ikpeazu ya fice daga helkwatar karamar hukumar ta Bende inda aka shirya liyafa ga tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Bende.

Harin na ofishin yansanda a Bende yazo ne kasa da mako guda bayan yan bindiga sun kone ofishin yansanda na kasuwar Ubani, duka a yankin karamar hukumar ta Bende.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

8 + 13 =