‘Yan bindiga sun kashe sojoji akalla 16 a jamhuriyar Nijar

260

Akalla sojoji 16 ne suka mutu a Jamhuriyar Nijar a karshen mako sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai musu a lardin Tahoua.

An kai harin ne a yankin da aka kashe fiye da fararen hula 200 a wani hari da babu wanda ya dauki alhakin kai shi a watan Maris.

Wasu masu dauke da makamai ne suka yi wa sojojin kwanton-bauna a kusa da garin Agando da ke yankin na Tahoua.

Sojoji 6 sun jikkata a harin kuma ba a san inda soja daya yake ba.

An rawaito cewa an kai sojojin da suka jikkata wani asibiti da ke yankin na Tahoua yayin da aka binne wadanda suka mutu a gaban jami’an gwamnati da na tsaro.

‘Yan bindigar sun yi awon gaba da motocin soji uku sannan suka lalata daya.

Yankunan Tillia da Tassara da ke lardin nan Tahoua sun kasance cikin dokar ta-baci tsawon watanni sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda a yankin da ke kan iyaka da kasar Mali.

BBC

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + eleven =