Sojoji a Mali sun kame shugaban kasa da firaminista da kuma ministan tsaro na gwamnatin rikon kwaryar kasar a jiya Litinin bayan an yi wa majalisar ministocin kasar garambawul.
Wasu majiyoyin diflomasiyya da na gwamnati sun tabbatar wa da manema labarai cewa ana tsare da shugaba Bah Ndaw, da Firaminista Moctar Ouane da ministan tsaro Souleymane Doucoure a wani sansanin soji.
An dorawa Ndaw da Ouane alhakin jagorantar zaben sabuwar gwamnatin farar hula cikin watanni 18 amma wasu da dama a cikin gwamnati da yan adawa na bayyana fargaba kan yadda sojoji suka mamaye manyan kujerun gwamnati.
Kamen na zuwa bayan sauya wasu daga cikin sojojin da suka jagoranci juyin mulki a watan Agusta a majalisar ministoci.