NABTEB ta saki sakamakon jarabawar Nov/Dec 2020

185

Hukumar jarabawar kasuwanci da fasaha (NABTEB) ta saki sakamakon jarabawar watan Nuwamba zuwa Disambar 2020.

Magatakardar hukumar, Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe, ta sanar da haka a yau a Benin, babban birnin jihar Edo.

Tace jumillar dalibai 32,514 ne suka yi rijistar zana jarabawar a cibiyoyi 1,583, amma dalibai 32,54 ne suka rubuta jarabawar.

A cewarta, daga cikin adadin dalibai dubu 32 da 336 da suka rubuta jarabawar, dalibai 21,175 sun samu kredit 5 zuwa sama, ciki har da Turanci da Lissafi.

Tace an rage satar jarabawar sosai a bana, ta hanyar amfani da dabarun tabbatar da inganci na hukumar, inda ta kara da cewa an samu dalibai 250 da laifin satar amsa, idan aka kwatanta da dalibai 603 da aka samu da laifin satar amsar a bara.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 14 =