
Jiragen yakin Isra’ila sun kai hari kan dogayen gine-gine da sauran gurare a Zirin Gaza daidai lokacin da Falasdinawan dake Zirin da ake fatattaka suka tashi a yau domin bikin Sallah karama ana tsaka da yi musu ruwan bama-bamai.
Tun bayan da Isra’ila ta fara luguden wuta a daren ranar Litinin, ma’aikatar lafiyar Gaza tace an kashe akalla mutane 86 ciki har da yara 17. Kazalika an raunata mutane 480.
An kuma kashe akalla mutane 6 ‘yan Isra’ila tare da wani dan Indiya guda.
Sojin Isra’ila sun ce an harba rokoki 100 daga Gaza zuwa gurare daban-daban a Isara’ila kuma sun kara tsaro a kusa da yankunan gabashin zirin Gaza.
An kuma yi munanan arangama tsakanin yahudawan Isra’ila da Falasdinawan dake Isra’ila a birane daban-daban cikin Isra’ila.
Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson, yace Birtaniya na san ganin an gaggauta kawo karshen rikicin.