Mataimakin shugaban kasar Mali Kanal Assimi Goita ya ce ya tsige shugaban kasar da firaminista saboda sun karya ka’idojin mika mulki ta hanyar rashin tuntubarsa kan sauye-sauyen majalisar ministocin kasar.
A shekarar da ta gabata, Kanal Goita ya jagoranci juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Ibrahim Boubaca Keïta. Ya hau mukamin mataimakin shugaban kasa a gwamnatin rikon kwarya wacce aka kafa domin share fagen komawa mulkin farar hula.
Assimi Goita ya ce za a yi zabe a shekara mai zuwa.
A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a saki shugaban kasar Mali Bah Ndaw da firaminista bayan rundunar sojan kasar ta kama tare da tsare su a wani sansanin soja da ke kusa da Bamako, babban birnin.
Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya yi kira da a kwantar da hankali cikin wani sakon Twitter.
Kungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka da Kasar Amurka duk sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.