Mahara sun ce masallata dake Sallar Tahajjud a Jibia

53

‘Yan fashin daji a jiya da tsakar daren suka sace masallata dake sallar Tahajjud a wani masallachi a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Lamarin ya auku a kusa da Abbatuwa dake garin Jibia.

Daya daga cikin jami’an kwamitin yan gudun hijira na Jibia, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai, yace yawan wadanda aka sace zai iya kaiwa 40.

Yace da misalin karfe 7 da rabi na dare a jiya Lahadi suka samu bayanan sirrin dake cewa ‘yan fashin daji na shirin kawo hari Jibia, inda suka sanar da jami’an tsaro da yan kato da gora.

Yace yan fashin daji sun jima suna kokarin kai hari Jibia inda wasu da aka kama suka jiyo su suna tattaunawa dangane da shirinsu na kawo hari garin.

Kakakin yansanda na Katsina, Gambo Isah, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace maharan sun zo dayawansu, inda suka zagaye masallatan a wani sabon masallachi dake wajen garin Jibia.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × five =