Kwamitin El-Rufai na neman a sayar da man fetur N385 kowace lita

9

Gwamnonin Najeriya suna so a mayar da farashin man fetur naira 385 duk lita daya.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kungiyar gwamnonin kasar ta fitar bayan kammala taronta ta internet a jiya da dare.

Sun yanke hukuncin ne bayan yin duba ga rahoton da wani kwamiti da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya jagoranta da ya goyi bayan janye tallafin mai daga gwamnati.

Rahoton na El-Rufa’i ne ya kuma bayar da shawarar a mayar da farashin man fetur din zuwa naira 385.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da Gwamnan Babban Bankin Kasa (CBN) Godwin Emefiele da Shugaban Rukunin Kamfanin NNPC, Mallam Mele Kyari.

A yayin gabatar da rahoton a wajen taron, Gwamna El-Rufa’i ya bayyana cewa duk wata gwamnati na kashe tsakanin naira biliyan 70 zuwa biliyan 210 kan tallafin man fetur, wanda ake sayar da litarsa a yanzu kan naira 162.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two + six =