Gwamnatin Tarayya tace ba ta gaggawar kara kudin man fetur

30

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva yace gwamnatin tarayya baza tayi gaggawar karin kudin man fetur ba.

Timipre Sylva ya sanar da haka lokacin da yake mayar da martani kan shawarar da kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayar na kayyade farashin Mai tsakanin naira 380 zuwa naira 408.5 kowace lita.

A taro ta internet a ranar Laraba, gwamnonin sun yi kiran da janye tallafin man gabadaya tare da barin kasuwa ta tsayar da farashi.

Inda suka ce baza a iya dorewa da biyan tallafin mai ba, kuma masu fasa kwauri da ‘yan kasuwar bayan fage ne kadai ke amfanuwa da shi.

Shawarar gwamnoni ya bata ran mutane a fadin kasarnan inda ‘yan Najeriya da dama ke cewa hakan zai kara yawan wahalhalun da ake sha a kasa.

Amma da yake mayar da martani, Sylva ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewa baza a kara kudin man ba a watan Yuni mai zuwa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 3 =