Gwamna Badaru ya yi alkawarin cigaba da biyan mafi karancin albashi

33
Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, yace jiharsa ba ta daga cikin jihoshin da ma’aikata ko ‘yan fansho ke bin bashin hakkokinsu, kuma yayi alkawarin dorewa da hakan.

Gwamnan ya sanar da haka a Dutse lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar ma’aikata ta duniya.

Gwamnan ya kuma yi alkawarin cigaba da biyan sabon mafi karancin albashi duk da karancin kudaden da ake samu daga tarayya a kowane wata na kason jiha da kananan hukumomi.

Yace gwamnatin jihar za ta biya albashi da fansho a watanni masu zuwa duk da gargadin cewa akwai yiwuwar kasa samun ko sisi daga tarayya saboda kudaden da ake biya wajen tallafin man fetur.

Gwamnan yace gwamnatinsa ta shiryawa halin tattalin arziki tare da kauracewa kashe kudade ba bisa tilas ba.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan kwadago ta kasa NLC a jihar Jigawa, Sanusi Alhassan, ya yabawa gwamnan bisa tabbatar da cewa ana biyan albashi da fansho akan lokaci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

sixteen − 6 =