El-Rufa’i ya kafe kan korar ma’aikata

38

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a jiya ya ce babu irin matsin lambar da za ta sa shi ya janye daga shirin sa na korar ma’aikata.

Gwamnan a bayanan da aka watsa, ya kuma sha alwashin neman hakki daga kungiyar kwadagon ta kasa (NLC) wacce ya zarge ta da take hakkin ‘yan jihar Kaduna a tsawon kwanaki uku da ta yi tana yajin aiki.

Gwamnan ya yi magana ne bayan da gwamnatin tarayya ta tsoma baki a rikicin da gwamnatin jihar ta yi da kungiyoyin kwadago wanda ya jawo rufe ayyukan tattalin arziki da walwala  tsawon kwanaki uku a jihar.

Daga baya bangarorin biyu sun sanya hannu a wata yarjejeniya a Abuja sannan an kafa wani kwamiti mai mambobi 10 don aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma.

Bangarorin sun kuma amince cewa NLC ba za ta ci gaba yajin aikin ba, yayin da babu wani ma’aikacin da gwamnatin jihar za ta hukunta saboda shigarsu yajin aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 + 16 =