Corona: Gwamnati ta ayyana neman wasu matafiya 90

15

Gwamnatin Tarayya ta bayyana wasu matafiya 90 da suka koma kasar daga Brazil da Indiya da Turkiyya a matsayin masu hadari bayan sun ki bin dokokin kariya daga cutar korona.

A cewar kwamitin yaki da korona, ana nemansu ne ruwa a jallo sakamakon sun ki kai kansu a yi musu gwajin cutar bayan sun isa kasar.

Mutanen sun kunshi ‘yan Najeriya 63 da ‘yan kasar waje 27 da suka sauka a ranakun 8 da kuma 15 ga watan Mayu.

Sun sauka ne a filayen jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas da kuma Nnamdi Azikiwe na Abuja.

Cikin wata sanarwa, kwamitin ya ce za a hukunta su ta hanyar dakatar da fasfunansu na tsawon shekara daya da hana su biza ko kuma soke izinin zama a Najeriya ga ‘yan kasar waje.

Ya kara da cewa suna kawo mummunar barazana ga lafiyar al’umma sakamakon kauce wa killace kansu na kwana bakwai da suka yi, wanda tilas ne ga duk wanda ya shiga Najeriya daga wasu kasashen waje.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − five =