Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi ayi addu’o’i domin magance satar mutane da fashin daji da yunkurin neman mulki ko ta halin kaka ta hanyar neman raba kasarnan.
Shugaban ya yi kiran cikin sakonsa na taya murna ga dukkanin ‘yan Najeriya da musulman duniya bisa bikin sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadan.
Shugaban kasa a sakon nasa wanda ya sanyawa hannu da kansa, yayi kiran a samu hadin kai tsakanin dukkan yan kasa musamman a wannan lokacin da kasarnan ke fuskantar kalubale daban-daban.
Yace za a magance matsalolin idan Najeriya ta cigaba da kasancewa a matsayin kasa daya.
A wani labarin kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yace yana sa ran ‘yan Najeriya su kasance masu hakuri sosai ga gwamnatinsa, dangane da karuwar rashin tsaro.
Shugaba Buhari, a sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya saki a jiya, ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su cigaba da kiyayewa da dokokin kariya daga corona tare da gudanar da bukukuwa cikin nutsuwa.
Shugaban kasar na shan suka sosai saboda kalubalen tsaro a kusan dukkan sassan kasarnan.
Bayan kungiyoyi daban-daban sun bukace shi da ya sauka daga mulki ko a tsige shi, gwamnonin kudancin kasarnan 17 a ranar Talata sun neme shi ya yiwa kasarnan jawabi dangane da karuwar rashin tsaro.
Daga cikin gwamnonin akwai wadanda aka zaba a karkashin tutar jam’iyyar APC.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kammala Sallar Idi a fadar shugaban kasa dake Abuja, shugaban kasar yace gwamnatinsa na yin iya kokarinta wajen tsare rayukan jama’a.
Ya kuma sha alwashin cewa gwamnatinsa za tayi amfani da kayan aiki da mayakan da take da su wajen magance ‘yan fashin daji domin tabbatar da cewa mutane na zuwa gonakinsu domin noman abinci a damina mai zuwa.