Buhari, Lawan, Magashi, Ndume sun yi jimamin mutuwar Attahiru

42

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kaduwa game da mutuwar babban hafsan sojin kasa Ibrahim Attahiru da sauran jami’an soji, yana mai cewa wadanda suka mutu ba za suyi mutuwar banza ba.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman Femi Adesina ya wallafa, Shugaba Buhari ya ce yayi matukar bakin ciki game da hatsarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Babban Hafsan Sojojin, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, da sauran jami’an soja.

Shugaban kasar ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu, da sojoji, da ma ‘yan Najeriya baki daya, yana mai bayyana su a matsayin gwaraza wadanda suka sadaukar da rayukansu domin samun zaman lafiya da tsaro a kasarnan.

Shugaban kasar yace hadarin babban koma baya ne ga kasarnan a daidai lokacin da sojojin Najeriya ke shirin kawo karshen kalubalen tsaro da kasarnan ke fuskanta.

Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran hafsoshin sojan sun mutu ne a wani hatsarin jirgin sama a jiya a wata ziyarar aiki da suka kai jihar Kaduna.

‘Yan Najeriya da dama na mayar da martani game da mutuwar hafsan sojojin da wasu a hadarin jirgin saman na jiya Juma’a.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa abin takaici ne mutuwar Attahiru, kimanin wata hudu bayan nada shi.

Bashir Magashi ya ce, mummunan hatsarin da ya lakume rayukan babban hafsan sojan, tare da wasu manyan hafsoshi da mataimakan sa, babbar asara ce ga kasarnan.

Bashir Magashi ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da hadiminsa na musamman kan yada labarai, Mohammad Abdulkadir, ya fitar a yau a Abuja.

Ya jajantawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sojoji da hukumar sojin kasa, musamman ma danginsa da kuma Najeriya baki daya.

Bashir Magashi ya bayyana marigayi Ibrahim Attahiru a matsayin jarumi mai da’a da kuma sadaukarwa wanda ya mutu a kan aikin domin cigaban kasarsa.

Hakazalika, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana mutuwar da marigayi Babban Hafsan Sojojin, Ibrahim Attahiru, da wasu hafsoshin soji 10 a wani hatsarin jirgin sama a jiya a matsayin gagarumar asara ga kasarnan.

Ahmad Lawan, a cikin wata sanarwa daga mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ola Awoniyi, a daren jiya, ya koka kan yadda wannan lamarin ya jefa daukacin al’ummar kasarnan cikin jimami.

Haka kuma, Shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar Dattawa, wanda kuma shi ne Sanata mai wakiltar gundumar Sanatan Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume a yau ya bayyana rasuwar marigayi Babban Hafsan Sojin, Ibrahim Attahiru, da wasu mutane 10, a matsayin abin takaici.

Sanatan, cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, ya koka da cewa marigayi janar din ya mutu ne a lokacin da al’umma dubansa domin samar da shugabancin da ya dace wanda zai kawar da tayar da kayar baya da sauran nau’ikan aikata laifuka a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 3 =