Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi kiran a mika mulki ga gwamnatin dimokradiyya a kasar Chadi nan da wata 18, biyo bayan karbe iko da soji suka yi a watan jiya.
Kungiyar ta AU ta fito karara ta nuna bata goyon bayan sojojin su kara jimawa kan mulki.
Kwamitin soji da ke jagorantar kasar yayi alkawarin gudanar da zabe cikin watanni 18 masu zuwa.
Mahamat Idris Deby, dan tsohon shugaban kasar da aka kashe Idriss Deby ne ke jagorantar kasar a yanzu, bayan kashe mahaifinsa da aka yi a watan jiya.
Ana ta fuskantar zanga-zanga akai-akai tun bayan da sojojin suka karbi mulki, an kuma kama gwamman ‘yan fafutuka a dalilin haka.