Mukaddashin gwamnan jihar Jigawa Mallam Umar Namadi ya rantsar da mai shari’a Umar M. Sadiq a matsayin alkalin alkalan jihar Jigawa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai jiya dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar shari’a ta jihar Jigawa, Zainab Baba Santali.
Wannan ya biyo bayan shawarwarin da Majalisar Kula da Harkokin Shari’a ta Kasa ta bayar da kuma karbar shawarar da Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya bayar.
Majalisar Dokokin Jiha ce ta tabbatar da nadin bisa tanadin kudin tsarin mulkin Najeriya.
Mai Shari’a Umar M. Sadiq shi ne Alkalin Alkalai na hudu na Jihar Jigawa, wanda ya gaji tsohon Alkalin Alkalai, Marigayi Honarabul Aminu Sabo Ringim wanda ya yi ritaya a ranar 25 ga Nuwamban 2020 kuma ya rasu a hatsarin mota kwanan nan. Umar M. Sadiq ya kammala karatun lauya ne aJami’ar Ahmadu Bello dake Zariya kuma ya fara aiki a matsayin lauya a shekarar 1989.